ABNA24 : Wani mai magana da yawun rundunar da ake kira da MINUSCA, Laftanar Kanar Abdoulaziz Fall, ya shaida wa kamfanin labarai na AFP cewa sojojin gwamnati da ke zaune a Mann sun fuskanci hari daga wata kungiya da ake kira 3-R (Return, Reclamation, Rehabilitation).
Kakakin ya ƙara da cewa baya ga waɗanda aka kashe ɗin har ila yau kuma an raunana wasu mutane da dama.
Sai dai kuma ya ce a halin yanzu dai lamurra sun lafa a garin na Mann da ke kimanin kilomita 550 daga babban birnin ƙasar, Bangui.
Ita dai wannan ƙungiyar ta 3-R na daga cikin ƙungiyoyin mayakan sa-kai da aka kafa su a ƙasar wacce ta ke ci gaba da fuskantar tashin hankali mai tsanani cikin shekarun goman da suka gabata.
342/