1 Agusta 2021 - 16:29
Kungiyar Tarayyar Turai Na Shirin Sanya Wa Lebanon Takunkumi

Kungiyar Tarayyar Turai ta fara shirin kakabawa wasu jami’an gwamnati da kuma wasu kungiyoyi a kasar Lebanon takunkuman tattalin arziki bayan da shugaban kasar ta Lebanon ya amincewa Najib Mikati ya kafa gwamnati.

ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani bayani wanda kwamitin tsara ayyukan kungiyar kasashen 27 ya fitar a jiya jumma’a.

Bayanin ya bayyana cewa takunkuman tattalin arzikin zasu hada da hana wasu daddaikun mutane, visar shiga kasashen na EU, ko kuma hana kamfanoni da mutanen kasashen hulda da su.

Har’ila yau bayanin ya kara da cewa akwai yiyuwan a kwace asusun ijiyar kudade da kuma kadarorin wasu mutane a kasar ta Lebanon wadanda suke kasashen na Turai.

Manufar takunkuman tattalin arzikin dai it ace takurawa yan siyasar kasar da kuma masu fada a ji, na su amincewa a sauya tsarin siyasar kasar don fitar da mutanen kasar daga matsalolin tattalin arziki da zamantakewa da suke fama da su.

342/