ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA ya bayar da rahoton cewa, a zaman da ‘yan majalisar dokokin kasar Iran suka gudanar jiya, sun cimma matsaya kan gudanar da taron rantsar da zababben shugaban kasar Ibrahim Ra’isi a ranar Alhamis mai zuwa.
Rahoton ya ce, Ra’isi zai yi ratsuwar kama aiki ne da misalign karfe 5 na yammacin ranar ta Alhamis, wanda taron zai gudana ne a zauren majalisar dokokin kasar ta Iran da ke birnin Tehran, tare da halartar ‘yan majalisa da kuma baki daga kasashe kimanin 50.
Haka nan kuma majiyar majalisar ta tabbatar da cewa, tuni aka dauki dukkanin matakan da suka dace na kiwon lafiya a taron, domin tabbatar da cewa an kiyaye dukkanin wasu matsaloli na kiwon lafiya a wurin a yayin taron.
Idan Ra’isi ya mika sunayen ministocinsa zuwa lokacin rantsar da shi, daga kwanaki biyu bayan rantsar da majalisar za ta fara zama domin yin dubi kan sunayen, bayan kammala yin dubi a kansu, za a gudanar da zama na tantancewa.
342/