28 Yuli 2021 - 15:01
Saudiyya Ta Kara Saka Wasu Sharudda Ga Masu Ayyukan Ibada Na Umarah

Gwamnatin kasar Saudiyya ta kara saka wasu sharudda ga masu ziyara na ayyukan ibada na Umrah daga kasashen ketare.

ABNA24 : Shafin yada labarai na jaridar Al-dastur ya bayar da rahoton cewa, mataimakin ministan ma’aikatar aikin hajji da Umra ta kasar Saudiyya Hesham saeed ya sanar da cewa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na karuwar barazanar cutar corona, sun kara wasu sharudda ga masu zuwa Umrah daga kasashen ketare.

Ya ce a halin yanzu akwai kasashen da gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa ‘yan wadannan kasashen ba za su iya zuwa kasar Saudiiya ba saboda dalilai na kiwon lafiya.

Ya ce wadanda suke bukatar zuwa aikin umrah daga wadannan kasashen, za su iya neman izinin shiga cikin kasar Saudiyya, daga kasashen da aka yarje musu shiga cikin kasar.

Ya ce hakan ya hada da neman visa da kuma tabbatar da cewa an samu rigakafin cutar corona na’in rigakafin da gwamnatin Saudiyya ta amince da shi a hukumance kafin shiga kasar.

Bay aga haka kuma, daga cikin sharuddan shi ne dole ne duk wanda ya shiga kasar, a duk lokacin da ya yi aikin ibada na Umrah, bayar ziyartar dakin Ka’abah da sa’io 6, dole ne ya kai kansa wajen jami’an kiwon lafiya, domin bincikar lafiyarsa.

342/