28 Yuli 2021 - 14:50
Tunusia : An Kafa Dokar Hana Fitar Dare Ta Tsawon Wata Guda

Shugaba Kais Saied na Tunusia, ya ba da umarnin sanya dokar hana fitar dare ta tsawon wata guda, kwana daya bayan da kasar ta shiga halin rashin tabbas sakamakon rusa majalisar dokoki da shugaban ya yi, tare da korar wasu ministocinsa.

ABNA24 : Dokar wacce ta fara aiki a cikin daren jiya, ta haramta zirga zirgar motoci da mutane tsakanin birane daga karfe bakwai na yamma har zuwa shida na safe, daga ranar 26 ga watan Yuli har zuwa 27 ga watan Agusta, in ban da wadanda aikinsu na wajibi ne ba.

Kasashen duniya da dama dai sun bukaci a kai zuciya nesa a kasar ta Tunusia.

Shi ma babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya nuna damuwa kan halin da ake ciki a Tususiar, inda ya yi kiran dukkan bangarorin biyu su sasanta banbance-banbancen da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi.

Matakin da Shugaba Kais Saied na Tunusia, ya dauka, na zuwa ne bayan shafe dogon lokaci na zamga zangar da ‘yan kasar ke yi, ta kiran gwamnatin kasar ta yi murabus saboda matsin tattalin arziki da kuma kasa shayo kan annobar korona.

342/