26 Yuli 2021 - 16:44
Iran Da Qatar Sun Sha Alwashin Karfafa Alakar Dake A Tsakaninsu

Ministan harkokin wajen kasar Qatar, Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, na wata ziyara a Tehran, mai manufar karfafa alaka tsakanin kasashen biyu.

ABNA24 : Yayin ziyarar tasa, Mohammed bin Abdulrahman Al-Thani, ya gana da takwaransa na Iran, Mohammad Javad Zarif, inda suka tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen da yankin dama kasa da kasa.

A daya bangaren kuma, ministan harkokin wajen Qatar din ya gana da zababben shugaban kasar Iran, Ebrahim Ra’isi.

Yayin ganawar Sayyed Ibrahim Ra’isi, ya bayyana cewa Iran da Qatar a matsayin 'yan uwan juna kuma abokan hadin gwiwa a yankin, wanda yana da mahimmanci su kara karfafa alakar dake tsakaninsu.

Samun tsaro da kwanciyar hankali a yankin na bukatar hadin kan kasashen yankin bisa amincewa da juna da kuma hana katsalandan daga kasashen waje," in ji Raisin.

Ministan na Qatar din a nasa bangaren ya ce, Qatar na neman hadin kai don karfafa alakar kasashen biyu da kokarin tabbatar da tsaron yankin.

342/