24 Yuli 2021 - 06:32
Palasdinu: Fiye Da Mutane 200 Sojojin Isara’ila Suka Jiwa Rauni A Jiya Jumma’a A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Jami’an tsaro na haramtacciyar kasar Isar’ika (HKI) sun jiwa palasdinawa kimani 200 rauni a jiyya jumma’a, a lokacinda suke zanga-zangar mako-mako da suka saba yi a duk ranar jumma’a, inda suke allawadai da gine-ginen da ake wa yahudawa a yankinsu da aka mamaye.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Wafa na falasdinawa ya bada rahoton cewa yahudawan sun farwa falasdinawa masu zanga zanga a yankin yamma da kogin Jordan wadanda suka hada da garin Nablus, Biitaa da kuma Jabal-Sabih, inda suka jiwa falasdinawa da dama rasuna. Daga cikinsu akwai mutane 146 a garin Nablusn.

Ahmad Jibril shugaban hukumar hilal Ahmar ko red cross a yankin ya fadawa kafafen yada labarai kan cewa an harbi mutane 33 da harsasai na gaskiya sannan wasu 87 saboda shakar hayaki mai sa hawaye sun shake.

342/