ABNA24 : Yayin tattaunawar bangarorin biyu sun tabo batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu dama halin da ake ciki a yankin dama kasa da kasa.
Shugaba Ruhani na Iran, ya bayyana cewa, a matsayin kasashen biyu masu karfi a yankin dama cikin kasashen musulmi suna da rawar da zasu taka domin shayo kan matsalolin dake faruwa a yankin.
Ya kara da cewa a bangaren alaka ta siyasa, tattalin arziki al’adu da batutuwan da suka shafi kasa da kasa kasashen biyu makobtan juna na da alaka mai kyau.
342/