ABNA24 : Bayan kammala sallar idin dai musulmai masu hali kan yanka dabbobin layya a wani nau'i na ibada.
Wannan dai shi ne karo na biyu a jere da musulmai ke gudanar da bukukuwan babbar sallah cikin yanayi na fama da annobar korona data addabi duniya, wanda ya sanya kasashe da dama suka takaita yanayin yadda aka saba gudanar sallar a shekarun baya.
Sallah'r layya dai na zuwa ne kwana daya bayan masu aikin hajji sun yin hawan dutsen Arafat, a ci gaba da aikace aikacen hajji, wanda a bana shi ma ya takaita ga mazauna Saudiyya 60,000 kawai.
Hukumomin Saudiyya dai sun takaita yawan masu aikin hajji saboda fargabar yaduwar sabbin nau’ukan cutar korona.
342/