13 Yuli 2021 - 11:21
​UAE Na Shirin Bude Ofishin Jakadanci A Tel Aviv A Ranar Laraba

Gwamnatin kasar hadaddiyar daular larabawa UAE, na shirin bude ofishin jakadanci a birnin Tel Aviv na Isra’ila a ranar Laraba mai zuwa.

ABNA24 : Jaridar Times ta Isra’ila ta bayar da rahoto a yau Litinin cewa, Gwamnatin kasar hadaddiyar daular larabawa UAE ta kammala dukkanin shirinta na bude ofishin jakadanci a birnin Tel Aviv na Isra’ila.

A rahoton kamfanin dillancin labaran sputnik, tun a cikin watan Janairun farkon wannans hekara da muke ciki ne ta 2021, Gwamnatin kasar hadaddiyar daular larabawa ta bude ofishin diflomasiyya a birnin Tel Aviv na Isra’ila, kuma tun daga lokacin har yanzu jami’an diflomasiyyar wannan kasa suna gudanar da aikinsu a cikin Isra’ila.

A karshen watan Yunin da ya gabata ne ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Isra’ila Yair Lapid ya jagoranci bude ofishin jakadancin yahudawan Isra’ila a birnin Abu Dhabi na UAE, inda aka gudanar da biki tare da halartar jami’an yahudawa da kuam na kasar ta hadaddiyar daular larabawa.

A ranar 15 ga watan Satumban shekarar 2020 da ta gabata ce dai aka rattaba hannu kan kulla alakar diflomasiyya tsakanin gwamnatin yahudawan Isr’ila da kuma kuma gwamnatin hadaddiyar daular larabawa a fadar White House da ke birnin Washington, inda tsohon shugaban Amurka Donald Trump ne ya dauki bakuncin rattaba hannun.

342/