ABNA24 : A cikin wani bayani da ya yi ga manema labarai a safiyar yau Juma’a bayan isar Tawagar Taliban a birnin Moscow na kasar Rasha, kakakin kungiyar ta Taliban Shahabuddin Dilawar ya sheda cewa, kungiyar Taliban za ta fatattaki ‘yan daesh daga cikin kasar Afghanistan.
Ya ce, a halin kungiyar ta kame kimanin kashi 85% na dukkanin kasar, in banda birnin Kabul fadar mulkin kasar da kewaye, wanda a cewarsa, suna tattaunawa da dukkanin bangarori kan yadda za a sake fasalin gwamnatin gwamnatin kasar.
Ko a ranar Laraba da ta gabata, an gudanar da wata tattaunawa wadda ministan harkokin wajen Iran Muhammad Jawad zarif ya goranta a birnin Tehran na kasar ta Iran, wadda ta hada wakilan kungiyar Taliban da na gwamnatin Afghanistan, da kuma wakilan kungiyoyi da jam’iyyu daban-daban na kasar ta Afghanistan, da nufin hada kan dukkanin bangarorin kasar wajen sama kasarsu mafita, ta hanyar yin aiki tare da juna.
Yanzu haka dai kungiyar ta Taliban ta kwace iko da daukacin iyakokin kasar, inda ta bayyana cewa ba ta da nufin cutar da kowace kasa daga cikin kasashe makwabta, kamar yadda kuma ba za ta cutar da al’ummar kasar Afghanistan, maimakon haka ma za ta hada kai da su ne baki daya, domin samun makoma mai kyau ga kasar.
342/