8 Yuli 2021 - 13:20
​Ramaphosa: Musulmi Sun Bayar Da Gagarumar Gudunmawa Wajen Yaki Da Wariya A Afirka Ta Kudu

Shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa suna alfahari da musulmi a kasar saboda sun taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar kasar.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, shugaban kasar Afirka ta kudu Cyrill Ramaphosa ya bayyana cewa suna alfahari da musulmi a kasar saboda sun taka muhimmiyar rawa wajen gina makomar kasar Afirka ta kudu.

Ramaphosa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake halartar wani taro na shugabannin musulmi da aka gudanar, domin yin dubi kan irin gudunmawar ad suke bayarwa wajen ci gaban al'ummar kasar, da kuma bangarorin da suke fuskantar kalu bale.

Ya ci gaba da cewa, baya ga irin rawar da musulmi suka taka tun lokacin yaki da wariyar launin fata a kasar, sun kuma bayare da gagaarumar gudunmawa wajen gina rayuwar jama'a a kasar, musamman ganin cewa musulmi a kasar Afirka ta kudu suna da arziki da dukiya, wanda hakan ya ba su damar gudunar harkokinsu cikin sauki.

Haka nan kuma Ramaphosa ya bayyana cewa, al'ummar musulmin Afirka ta kudu suna taimakon talakawa da marassa galihu tare da gudanar da ayyuka na jin kai, inda ya bayar da misali da abin da musulmi suka yi na taimakon al'umma a kasar a lokacin bullar cutar corona, Ramaphosa ya ce musulmi wani babban bangare ne da yake a matsayin jigoa cikin al'ummar Afirka ta kudu.

342/