8 Yuli 2021 - 13:16
​Iran:Shirin Bude Cibiyar Musayar Bayanai Dangane Da Tsaro A Tekun India Da pacific Ya Kusan Kammala

Babban kwamandan dakarun ruwa na kasar Iran ya bayyana cewa an kusan kammala aikin gina cibiyar musayar bayanai na tsaron tekunan Indiya da pecific a yankin Sistan Buluchistan na kudancin kasar Iran.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya nakalto Adminral Husain Khanzadi ya na fadar haka a yau Laraba a lokacinda ya kai ziyara a cibiyar musayar bayanan da ake kan kammalawa a Cabahar na kudancin kasar.

Admiral Khanzadi ya kara da cewa manufar bude wannan cibiyar ita ce tabbatar da tsaron ruwayen yankin da kuma na cikin gida. Ya ce za’a samar da wani tsarin musayar bayanai daga jiragen ruwa na yaki ko na daukar kaya da fasinja don sanin saunin yaniyi da kuma hatsura da ke iya faruwa a cikin ruwa na takunan yankin da na ruwan kasa da kasa. Admiral Khanzadi bai bayyana lokacinda da za’a bude cibiyar ba, amma ya ce an kammala mafi yawan ayyukan cibiyar.

342/