7 Yuli 2021 - 14:10
Rabi’i : Akwai Ci Gaba A Tattaunawar Saudiyya Da Iran

Iran ta bakin kakakin gwamnatin kasar, Ali Rabi’i, ta ce za ta ci gaba da tattaunawa da kasar Saudiyya har sai an samu sassaucin sabanin dake tsakaninsu.

ABNA24 : Muna tsamannin tattaunawa, musamman tsakanin al’ummar musulmi, ita ce hanya mafi dacewa wajen magance duk wani sabani’’ a cewar Ali Rabi’I, yayin taron manema labarai na mako mako da ya gudanar ranar Talata.

Ya kara da cewa a tattaunawar da akayi tsakakin bangarorin biyu, kawo yanzu an tabo tsabanin dake akwai tsakanin kasashen biyu cikin aminci, kuma an samu ci gaba, duk da cewa akwai akan fuskanci ‘yar tsarkakiya game da wasu batutuwan, wanda kuma yakan dauki lokaci.

Amma ya ce Iran, ta yaba da tattaunawar, tare da fatan ci gabanta har sai an samu warware dukkan sabanin dake akwai, ta hanyar girmamawa da mutunta bukatun ko wanne bangare, inji kakakin gwamnatin kasar ta Iran.

342/