ABNA24 : Wannan bayyanin ya fito ne yayin wata zantawa ta wayar tarho da bangarorin biyu sukayi a jiya Litini.
Yayin zantarwar shugaba Assad, ya taya zababen shugaban kasar ta Iran, Ibrahim Ra’isi murna kan zaben da aka yi masa a zaben shugabancin kasar Iran.
Ya kuma yi masa fatan samun nasara wajen aiwatar da aikin da yake shirin karba nan gaba.
Bangarorin kuma sun ce yana da mahimmanci su karfafa alaka tsakaninsu ta dukkan bangarori.
342/