5 Yuli 2021 - 13:24
Zababben Shugaban Iran Da Firaministan Pakistan Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Zababben Shugaban kasar Iran Ebrahim Ra’isi ya tattauna da firaminsitan kasar Pakistan, Imran Khan, inda suka tattauna kan batutuwa da dama.

ABNA24 : Bangarorin biyu sun sha alwashin karfafa alakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma sun amince kan kara bunkasa hadin gwiwar da ke akwai, musamman ta fuskar tattalin arziki.

Shugaban kasar Iran mai jiran gado ya nuna damuwarsa game da halin da ake ciki a Afghanistan, yana mai cewa, "Tsaron Afghanistan yana da muhimmanci a gare mu.

Shi ma dai Imran Khan da ya tabo batun Afganistan, ya yi gargadin cewa sabbin abubuwan da ke faruwa na iya haifar da mummunan sakamako ga Pakistan da Iran.

Dukkanin shugabannin sun amince cewa rashin zaman lafiya a Afghanistan zai haifar da kwararar ‘yan gudun hijira zuwa yankunan kan iyakar kasashen biyu.

342/