ABNA24 : Sama da mutane dubu 400 ne ke bukatar tallafin gaggawa a yankin da aka kwashe watanni takwas ana gwabza yaki.
Mukadashin sakataren kula da ayyukan jin kai na MDD, Ramesh Rajasingham, ya bayyana a taron farko na kwamitin tsaron MDD kan batun yankin na Tigray, cewa yankin ya shiga wani hali na rashin tabbas tun bayan da mayakan dake goyan ‘yan a ware suka kwace babban birnin jihar na Mekele a ranar Litini.
Baya ga hakan kuma an rusa wasu gadoji biyu masu matukar mahimmanci wajen isar da kayan agaji a yankin.
342/