ABNA24 : A cikin sakon, da ya aike shugaba Ruhanin, ya taya Gholam-Hossein Mohseni-Ejei murnar nadin da jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatollah Khamenei ya yi masa.
‘’Nadin da Jagoran ya yi ma ka a matsayin babban alkali, ya nuna kwarewarka a bangaren ayyukan shari'a. " inji shugaba Ruhanin.
A safiyar yau Alhamis ne ofishin jagaran juyin juya halin musulinci na Iran, ya sanar da nadin Gholam-Hossein Mohseni-Ejei, a matsayin sabon alkalin alkalai na kasar.
Gholam-Hossein Mohseni-Ejei, ya maye gurbin Ibrahim Ra’isi, wanda ya lashe zaben shugabancin kasar ta Iran da aka gudanar a ranar 18 ga watan Juni da ya shige.
342/