ABNA24 : Rahotonni sun tabbatar da cewa, wani bayahude ne mai tsatsauran ra'ayi ya fara watsa mata fenti a fuskarta tare da cin zarafinta a unguwar Hayyi Sheikh Jarah da ke birnin Quds, kafin daga bisani kuma 'yan sandan yahudawa suka kama ta suka tafi da ita. Ko a yau sojojin yahudawan sun kashe wata mata likita bafalastiniya, a lokacin da take tafiya da motarta a kudancin birnin Quds, bisa hujjar cewa tana da shirin taka sojojin Isra'ila ne da motarta, inda suka bude mata wuta, lamarin da yasa motar ta fita daga kan titi ta yi karo da tarin kasa, kuma a nan take ta rasu. Wasu daga cikin sojojin Isra'ila sun ce matar ta yi kure ne, inda ta bi hanyar da sojoji suka hana sauran motoci ratsawa saboda dalilai na tsaro, saboda haka sun bude wuta a kanta ne a lokacin da ta ratsa a kan wannan titi da aka hana motoci gittawa a kansa.
342/