ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Sayyid Riza Mazhari ya na fadar haka a safiyar yau Litinin a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa cibiyar tana cikin samar da alluran riga kafin cutar ta korona har miliyon 11 a ko wani wata nan da wata guda.
Mazhari ya kammala da cewa a halin yanzu cibiyar tana jiran ma’aikatar kiwon lafiya na kasar ta bada izinin fara amafana da alluran, kafin a fara yiwa mutanen kasar.
An fara gwajin alluran riga kafin cutar korona kirar masana a cikin kasar Iran ne a ranar 29 ga wata Decemban shekara ta 2020. Bayan kammala dukkan gwaje-gwajen da suka zama wajibi, a halin yanzu an fara yiwa mutanen kasar alluran riga kafin cutar ta korona samfurin kov-Irab Barakat a cikin kasa.
342/