ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Araqchi ya na fadar haka a jiya a taron dawo da Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA a birnin Vienna, ya kuma kara da cewa Iran ta na kan bakanta, na cewa dole ne Amurka ta dage mata dukkan takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata dangane da yarjejeniyar ta JCPOA sannan a bata lokaci na tabbatar da cewa an dage takunkuman da gaske a sannan ne za ta koma kan inda take na mutunta yarjejeniyar.
Ana Saran wannan zagaye na tattaunawa zai zama na karshe ko kuma kusa da na karshe kan wannan batun.
342/