ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press(IP) na kasar Iran ya nakalto Khadib Zadeh yana fadar haka a jiya Jumma’a a shafinsa ba twitter, inda yake maida martani ga matakin da ma’aikatar baitul mali ta kasar Amurka ta dauka, na soke takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa wasu jami’an gwamnatin kasar Iran guda 3 don sun bar mukaman da suke rike da su.
Amma a lokaci guda baitul malin ta dora sabbin takunkuman tattalin arziki kan wasu Iraniwa, wadanda take riya cewa suna taimakawa mayakan Huthi na Yemen, wadanda suke kare kasarsu daga mamayar kasar Saudiya tun shekara ta 2015.
A yau Asabar ce 12 ga watan Yuni, za’a koma kan teburin tattaunawa a birnin Vienna na kasar Austria, tsakanin Iran da kasashe 4+1 dangane da shirin maido da Amurka cikin yarjejeniyar JCPOA, da kuma dagewa kasar Iran takunkuman Zaluncin da Amurkan ta dora mata.
342/