9 Yuni 2021 - 19:53
Iran Da OPEC Sun Tattauna Kan Batun Kasuwar Man Fetur A Duniya

Wakilin Iran a kungiyoyin kasa da kasa dake Vienna, ya gana da sakatare janar na kungiyar kasashen masu arzikin man fetur ta duniya, domin sanin inda aka kwana game da kasuwar man fetur a duniya.

ABNA24 : A wani sakon Tuwita da ya wallafa, Jami’in na Iran, Kazem Gharibabadi, ya ce ya yi ganawa mai armashi tsakaninsa da sakatare janar na kungiyar ta OPEC, Mohammed Sanusi Barkindo, kuma sun tabo batutuwa da dama da suka shafi kasuwar ta man fetur a duniya.

Ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake tsamanin dawowar Iran, a kasuwar man fetur.

Kafin hakan dama ministan man fetur na kasar ta Iran, Bijan Zanganeh, ya bayyana a taron bidiyo na ministocin man fetur na kasashen mambobin kungiyat ta OPEC da aka gudanar a ranar 1 ga watan Yuni cewa an tattauna kan batun dawowar Iran a hada hada kasuwancin man fetur na duniya.

342/