ABNA24 : Rahoton ya ce cibiyoyi da kungiyoyin musulmi daban-daban gami da kwamitin limaman masallatan kasar, da kuma kungiyoyin bayar da agaji na musulmi da kuma bankin musulunci na kasar Kenya ne suka harhada taimakon.
Abubuwan da aka tara dai sun hada da abinci da kuma sauran kayayyakin bukatar rayuwa, baya ga haka kuma sun hada kudade fiye da dala miliyan biyu ta Amurka, a matsayin taimakon farko da suka fara tattatara domin taimakon wadanda suka rasa kaddarorinsu da iyalansu sakamakon hare-haren Isra'ila a Gaza.
A tsawon kwankin da Isra'ila ta kwashe tana kaddamar da hare-hare a kan al'ummar Gaza, al'ummar musulmi na kasar Kenya har ma da wadanda ba musulmi ba, sun yi ta gudanar da zanga-zangar yin tir da Allawadai da hakan, tare da kiran al'ummar duniya da su takawa yahudawa burki kan kisan kiyashin da suke yi kan al'ummar Falastinu.
342/