8 Yuni 2021 - 10:38
Jagoran Juyin Musulunci Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Hujjatul –Islam Ali Akbar Muhtashimi

Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Imam Ali Khamnei ya yi ishara da hidamar da marigayin Muhtashimi Pur ya yi wa juyin musulnci da jamhuriyar musulunci haka nan raunukan da ya samu saboda harin ta’addancin da makiya su ka kai masa.

ABNA24 : Wani sashen na ta’aziyyar jaoran ta kunshi cewa; Muhtashimi Pur ya kare rayuwarsa ne akan tafarkin daga tutar musulmi sama, haka nan juyin juya halin musulunci da kuma kare birnin kudus ta fafutuka wajen ‘yanto da masallacin Kudus da kuma taimakawa wadanda aka zalunta a duniya.

Daga cikin mukaman da ya rike a baya da akwai ministan harkokin cikin gida daga 1985-1989, ya kuma wakilci birnin Tehran a majalisar shawarar musulunci ta Iran a zango na uku da shida. Har ila yau ya zama mai bai wa shugaban kasa shawara akan harkokin zamantakewa daga 1997-1999.

An kwantar da Hujjaytul-Islam Ali Akbar Muhtashimi Pur ne a asibitin Khatamul-Anbiya bayan da ya kamu da cutar corona, ya kuma rasu a yau Litinin yana dan shekaru 75.

342/