31 Mayu 2021 - 12:50
An Gano Cewa Alluran Riga Kafin Cutar Korona Ta Coviran–Barekat Na Da Inganci Sosai

Jami’an kiwon lafiya a kasar Iran sun tabbatar da cewa alluran riga kafin cutar Korona wanda Aka samar a cikin gida ta na da inganci kamar sauran alluran riga kafin da ake amfani da su a sauran kasashen duniya a halin yanzu.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP ) ya nakalto shugaban kamfanin kera magunguna na Barakata Minoo Mohraz tana fadara haka, ta kuma kara da cewa Coviran ta na ta inganci kamar sauran alluran riga kafin da aka samar a sauran kasashen duniya, sannan ta na bada karariya daga kamuwa da cutar har zuwa kashi 80%. Banda haka alluram bai da wasu illoli da take jawowa, ko da ciwon kai ne idan an yiwa mutum alluran.

Minoo Mohraz ta kammala da cewa Coviran ta fi Sinopharm na kasar Cana karfi da inganci wajen bada kariya daga cutar ta Korona.

342/