ABNA24 : Sakon na shugaban kasar Iran ya kuma kunshi jinjinawa kasar Syria, akan yadda ta yi nasarar gudanar da zaben, tare da bayyana cewa; yadda al’ummar su ka fito kwansu da kwarkwatarsu yana a matsayin wani ci gaba ne akan hanyar ci gaban kasar.
Har ila yau, shugaban kasar na Iran ya bayyana gamsuwarsa da cewa alaka a tsakanin kasashen biyu za ta kara bunkasa fiye da kowane lokaci a baya.
Shi ma shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran Qalibaf, ya aike wa da shugaban kasar ta Syria nashi sakon na taya murna akan sake lashe zaben.
Qalibaf ya ce; Yadda al’ummar kasar su ka fito kwansu da kwarkwatarsu su ka yi zabe, duk da yadda kasar ta Syria take fuskantar matsin lamba, wata gagaruwar nasara ce.
342/