ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto shugaban yana fadar haka a safiyar yau Alhamis a birnin Kigali babban birnin kasar Ruwanda inda aka gudanar da taron juyayin kisan mutane kimani 250,000 a wata makabarta a birnin.
Kafin haka dai bincike daban-daban sun tabbatar da cewa sojojin kasar Faransa wadanda suke aiki a karkashin rundunar MDD a kasar Ruwanda a lokacin sun tabbatar da cewa za’a yi wannan kisan kiyashin, kuma suna da ikon hana yin hakan, amma basu dauki wani mataki ba, har aka yi kisan kiyashin.
Banda haka gwamnatin kasar Faransa ta lokacin karkashin shugabancin François Mitterrand ta ci gaba da goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda ta lokacin wacce ta jagoranci kisan mutane kimani 800,000 tsakanin kabilun Hutu masu rinjaye da tutsi tsiraru..
Wasu masana sun bayyana cewa afwan da shugaba Macron ya nema bai wadatarba don har yanzun akwai wasu wadanda ake zargi da hanu a kissan kiyashin akalla 47 wadanda suke samun mafaka a kasar Faransa. Emanuel Macron ya isa birnin Kigali a safiyar yau ALhamis, inda zai yi ziyarar aiki na kwanaki biyu.
342/