ABNA24 : Mista Jonathan, zai tattauna ne da sojoji da kuma wakilan kungiyoyin fara hula da kuma wasu manyan jami’an kasar, da zumar lalubo bakin zaren warware halin da kasar ta shiga bayan dakatar da aikin shugaban rikon kwarya na kasar da kuma firaministansa, lamarin da tuni wasu kasashen duniya irinsu faransa suka danganta da juyin mulki cikin juyin mulki.
Har yanzu dai babu cikakken bayyani game da shugaban rikon kwaryar na Mali Bah N'Daw, da firaminista Moctar Ouane, da sojojin ke tsare da a barikin sojin Kati.
A jiya dai jagoran sojin da suka yi juyin mulki a kasar a shekarar da ta gabata, Kanar Assimi Goita ya sanar da rushe gwamnatin rikon kwaryar kasar.
Bayanai daga kasar sun ce, wannan mataki ba zai rasa nasaba da rashin amincewar tsohon kwamitin ceton jama’ar kasar (CNSP) ba, biyo bayan cire mambobinta biyu, wato kanar Sadio Camara, tsohon ministan tsaro, da kuma kanar Modibo Kone, daga cikin sabuwar gwamnatin da firaministan ya kafa.
342/