ABNA24 : Har ila yau ministan tsaron na kasar Italiya da masu masaukin bakinsa, sun tattauna akan fasakwaurin makamai da na mutane da muggan kwayoyi a tsakanin yankin na yammacin Afirka zuwa nahiyar turai.
Guerini ya jaddada wajabcin yin aiki tare a tsakanin kasar tashi da yankin Sahel domin tabbatar da tsaro a yankin na yammacin Afirka.
Kasar Italiya tana da sojoji a karkashin rundunar MDD ta zaman lafiya da take girke a kasar Mali.
342/