20 Mayu 2021 - 14:18
An Samu Kyakkyawan Ci Gaba A Tattaunawar Vienna_ Araqchi

Mataimakin ministan harkokin wajen Iran, kana mai wakiltar kasar a tattaunawar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, ya ce an samu kyakkyawan ci gaba a tattaunawar Vienna.

ABNA24 : Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ‘’an samu ci gaba a tattaunawar da aka kwashe makonni biyu anayi, kuma an cimma ababe da dama.

Saidai a yanzu bangarorin da ke halartar tattaunawar zasu koma gida domin tuntuba game da wasu batutuwa da suka rage dake bukatar dogon nazari.

Muna fatan cimma fatan cimma matsaya a zagaye na gaba na tattaunawar a cewar Abbas Araqchin.

Batun dage wa Iran takunkuman da tsohuwar gwamatin Donald Trump na Amurka ya kakaba ma ta da kuma sake dawowar Amurka a cikin yarjejeniyar ta 2015 na daga cikin manyan batutuwan da suka mamaye ajandar tattaunawar ta Vienna.

342/