ABNA24 : A rahoton da tashar Almayadeen ta bayar, dakarun Qassam bangaren soji na kungiyar Hamas sun kai wani harin kwantan bauna a yau a kan wata motar bas da take daukar sojojin yahudawan Isra’ila yankin zirin Gaza.
Rahoton ya ce, jim kadan bayan faruwar lamarin, wasu tankokin yankin Isra’ila suka turnuke wurin da hayaki, domin kada kamarori su iya daukar hakakinanin abin da ya faru da sojojin yahudawan.
Baya ga haka kuma da yammacin yau Alhamis, dakarun an Qassam da ma wasu kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza, sun harba makamai masu linzami a kan wasu yankuna da Isra’ila ta mamaye, inda ta tsugunnar da yahudawa ‘yan share wuri zauna, wanda shi ma Isra’ila tana ci gaba da yin rufa-rufa kan hakan.
A nasa bangaren a cikin wani bayaninsa da ya gabatar a yau dangane da halin da ake ciki a yakin da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar Falastinu, Shugaban kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ta Hamas Isma’il Haniyya ya bayyana cewa, Isra’ila ta raina karfin da kungiyoyin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya suke da shi, amma bayan kaddamar da yakin da ta yi a yanzu ta fahimci sabanin abin da take tunani a baya.
342/