ABNA24 : Sannan a yau talata ana sa ran taron zai bukaci manya-manyan kamfanonin kasashen duniya su zuba jari a kasar ta Sudan bayan kaurace mata da suka yin a fiye da shekaru 30 da suka gabata.A ranar Lahadin da ta gabace shuwagabannin kasar Sudan suka isa birnin Paris na kasar Faransa don halattan taron kasa da kasa na kwanaki biyu don tallafawa gwamnatin rikon kwara ta kasar.
Jaridar Sudan Trinbune ta kasar Sudan din, ta bayyana cewa firai ministan kasar Abdallah Hamduk ya jagoranci tawaga ta farko zuwan taron, a yayins ashugaban majalisar koli ta mulkin kasar Abdel Fattah Albuhan ya jagoranci tawaga ta biyu zuwa taron.
Ministan harkokin wajen kasar ta Sudan Mariam Al-Mahdi ta bayyana cewa a halin yanzu an cire kasar Sudan daga cikin jerin kasashen da suke tallafawa ayyukan ta’addanci a duniya don haka babu wani tsaro ga kamfanonin kasashen duniya idan sun zuba jari a kasar Sudan
342/