13 Mayu 2021 - 18:50
Shugaban Kasar Iran Rauhani Ya Yi Kira Ga Dukkanin Bangarorin Siyasa Da Su Shiga A Yi Zabe Da Su

A yau Alhamsi ne dai shugaban kasar Iran ya yi kira ga dukkanin bangarorin siyasa ma’abota mahanga daban-aban da su shiga cikin zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa da za a yi nan gaba kadan.

ABNA24 : Shugaban kasar na Iran ya kuma bayyana cewa; Ranar karamar sallah, rana ce mai cike da albarka da tsarkaka daga zunubai, wacce bayan fitar da zakkar fidda kai da yin sallar idi ake son yawaita ambaton Allah.

Dr. Hassan Rauhani ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake kaddamar da wasu muhimman ayyuka na raya kasa ta hanyar bidiyo daga nesa da za su taimaka wajen samarwa da dubban mutane aikin yi.

Har ila yau shugaban kasar ta Iran ya yi fatan cewa zaben da za a yi zai kasance mai kyawu ga dukkanin al’ummar Iran.

342/