ABNA24 : Jiya Litini ne ya kamata a gudanar da taron, saidai aka dage shi har zuwa yau Talata.
Taron dai na da matukar mahimmanci ga kasar ta Chadi, don kuwa a yayinsa ne tawagar kwararu ta kungiyar AU din, za ta gabatar da rahoton binciken data gudanar kan tsarin kafa gwamnatin rikon kwaryar soji da aka kafa bayan mutuwar shugaba Idriss Deby, dama majalisar rikon kwaryar soji da aka kafa wacce dan mirigayin ke jagoranta tare da gwamnan janar janar din soji.
A yayin taron kungitar ta AU, za ta dauki mataki na ko ta sanya takunkumi kan Chadin ko kuma a’a, sakamakon karbar mulki sabanin yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.
Duka dai wannan matakin za’a dauke shi ne gwarwadon rahoton da tawagar ta AU, data kwashe tsawon kwanaki a Ndjamena za ta gabatar.
342/