ABNA24 : Tashar talabijin ta Aljazeera ta bayyana cewa gwamnatin yahudawan sahyoniyya sun bawa wasu yahudawan ‘yan share wuri zauna damar shiga yankin a kokarin da suke yin a korar falasdinawa daga gidajensu a wannan yankin da nufin maye gurbinsu da yahudawan da suka shigo da su daga kasashen waje.
Labaran ya kara da cewa majalisar dokokin Kenest ta yahudawan ta nuna goyon bayanta na korar Falasdinawa daga gidajensu, amma wasu yan tsirarun yan majalisar larabawa sun je unguwar don taimakawa falasdinawa mazauna yankin, saboda hana yahudawan korarsu daga gidajensu.
Gwamnatin HKI tana da shirin korar dukkan larabawa mazauna birnin Qudus don maida shi ta yahudawa zalla.
A wani labara da dumin duminsa mayakan Falasdinawa ta azzuddin kassam sun cillo makamai masu linzami 3 a kan birnin Qudus don nuna goyon bayansu ga falasdinawa da suke fafatawa da yahudawan a masallacin al-aksa da kuma wasu wurare a birnin.
342/