ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar hadin gwiwa ta yaki da ta’addanci a kasar Iraki Manja Janar Yahya Rasul ya sanar da cewa, sun samu nasarar cafke wasu manyan ‘yan ta’addan Daesh su biyar, daga ciki harda wani babban kasurgumi daga cikinsu da ake nema.
Ya ce rundunar ta fara kaddamar da farmaki a cikin larduna uku na kasar domin farautar mayakan kungiyar daesh da suka rage tare da murkushe su, inda ya ce ana samun gagarumar nasara a yayin farmakin, sakamkon hadin kan da jami’an tsaron suke samu daga al’umma.
Manja janar yahya Rasul ya ci gaba da cewa, ana kaddamar da wannan farmaki ne a yankunan Falluja da ke cikin lardin Anbar, sai kuma wasu yankuna na lardin Kirkuk, da kuma wasu yankuna da suke cikin lardin Bagadaza.
Ko a jiya jiragen yakin Iraki sun samu nasarar ragargaza wasu sansanonin mayakan ‘yan ta’adda na Daesh a arewacin kasar, inda wasu daga cikinsu suka halaka, wasu kuma suka jikkata, kamar yadda aka ragargaza makaman da suka girke a wadannan sansanoni.
Kasar Iraki dai ta fara fuskantar barazanar ‘yan ta’addan daesh ne tun daga lokacin kafa kungiyar a shekara ta 2014, wadda wasu kasashen larabawa suka dauki nauyin kafa su da kuma biyan kudaden horar da su da nufin mamaye kasar Iraki, kafin daga bisa aka karkata akalarsu zuwa kasar Syria.
342/