9 Mayu 2021 - 14:04
Falasdinawa Sun Bukaci Taron Kwamitin Tsaro Na MDD Da Gaggawa Dangane Da Qudus

Gwamnatin Falasdinawa mai cin gashin kanta ta bukaci kwamitin tsaro na MDD ya kira taron gaugawa don tattauna batun abinda ke faruwa a birnin Qudus.

ABNA24 : Jaridar Al-qudsul- Arabi ta nakalto Riyadhul Maliki ministan harkokin waje na gwamnatin Falasdinawan ya na fadar haka, ya kuma kara da cewa ma’aikatarsa ta gabatar da bukatu ga kungiyoyi da dama, wadanda suka hada da ta kasashen Larabawa, da kungiyar kasashen Musulmi da kuma kwamitin tsaro na MDD don gudanar da taron gaggawa kan ta’asar da sojojin haramtacciyar kasar Isara’ila take aikatawa kan al-ummar Falasdinu a birnin Qudus.

Maliki ya kara da cewa gwamnatin sa za ta bukaci wadannan kungiyoyin, bayan taronsu, su yi allawada da cin zarafin bil’adama, da kuma nuna wariya wanda Isra’ila take yi a Falasdinu, musamman a birnin Qudus. Banda haka zata bukacesu su yanke hulda da haramtacciyar kasar.

Labarin ya kara da cewa a cikin makonnin da suka gabata jami’an tsaron yahudawan sun raunata falasdinawa akalla 205 sannan sun kai wasu ga shahada.

Sannan a unguwar Sheikh Jarrah na birnin Qudus kuma sun yi kokarin fitar da Falasdinawa daga gidajensu don bawa yahudawa wadanda suka yo hijira zuwa kasar gidajensu.

342/