ABNA24 : Jaridar Al-Akhbar ta kasar Lebanon ta bayyana a safiyar yau Laraba kan cewa sojojin kasar ta Yemen sun sami nasara a kan sojojin Hadi a yankin Almeel dake arewacin lardin na Maarib inda suka kashe ko raunata mayakan hadi, kuma sun kama sansanonin mayakan nashi da dama.
Watannin ukku kenan da suka gabata ake fafatawa tsakanin sojojin kasar Yemen da kuma mayakan abdurabbu Mansur Hadi wadanda suke samun goyon bayan kasar saudiya da kawayenta.
A ranar 15 ga watan Maris na shekara ta 2015 ne saudia ta fadawa kasar Yemen da yaki da nufin maida tsohon shugaban kasan da yai murabus kan kujerar shugabancin kasar.
342/