ABNA24 : Bugu da kari sanarwar ta kara da cewa wani soja daya ya bace sanadiyyar harin na masu dauke da makaman.
Sakataren gwamnatin gudumar ta Tahoua Ibrahim Miko ne ya sanar da haka ta kafar talabijin, inda kuma ya halarci jana’izar kwamandan sojojin da aka kashe, laftanar Mamman Namewa.
Yankin dake kan iyakar Nijar da kasashe Mali da Burkina Faso yana daga cikin wuraren da masu dauke da makamai suke yawaita kai hare-hare tun daga 2012.
342/