ABNA24 : Rahotannin sun ce ɗaruruwan masu zanga-zanga ɗin ne suka fito kan titunan birnin Ramallah da ke Yammacin Kogin Jordan don nuna rashin amincewarsu da matakin jirkirta gudanar da zaɓen da Abbas ya ɗauka. Masu zanga-zangar dai suna ɗāuke da kwalaye da kuma tutar Falasɗinun suna rera taken cewa suna fatan ganin an kafa halaltacciyar gwamnati.
Har ila yau a Zirin Gaza ma dai ɗaruruwan mutane ne suka fito don yin Allah wadai da matakin da shugaba Abbas ɗin ya ɗauka.
Ita ma a nata ɓangaren ƙungiyar Hamas ta bayyana wannan mataki na Abbas ɗin a matsayin wani juyin mulki, tana mai cewa an ɗau wannan matakin ne don cimma wata manufa wacce ba ta da alaƙa da al’ummar Falastinu.
A safiyar yau Juma’a ce dai shugaban Falastinawan Mahmood Abbas ya sanar da jinkirta gudanar da zaɓen wanda aka shirya gudanar da shi a wata mai kamawa sannan kuma shi ne na farko cikin shekaru 15 ɗin da suka gabata yana mai cewa yayi hakan ne sakamakon matakin da Isra’ila ta ɗauka na hana Falastinawa da suke Gabashin Кudus shiga zaɓen.
342/