ABNA24 : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wata kungiya wacce ake kira ‘Force of the Karen National Union (KNU)’ ta bada sanarwan kwace sansanin sojojin kasar dake lardin Karen kusa da kogin Karen daga gabacin kasar a safiyar yau Talata.
Labarin ya kara da cewa kungiyar yan tawaye ta KNU ita ce kungiyar ‘yan tawaye mafi girma a kasar kuma bullarta a wannan karon ya zo ne a dai-dai lokacinda sojojin kasar suka kifar da gwamnatin democdiyya a kasar.
Labarin ya kara da cewa an kashe sojojin Myanmar da dama a sansanin, sannan mutanen ‘yankin sun kauracewa gidajensu don jin tsorin irin maida martanin da sojojin masu juyin mulki za su yi.
342/