ABNA24 : Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da gwamnatin kasar Sudan ta fitar a jiya, ta bayyana cewa kungiyar tarayyar Afirka za ta iya taka rawa wajen ganin an kawo karshen takun saka da ake yi kan batun madatsar ruwan ta Annahda, tsakanin Habasha da kuma gwamnatocin Masar da Sudan a daya bangaren.
Bayanin ya ce a cikin kwanaki masu zuwa, ministar harkokin wajen kasar Sudan Maryam Sadiqul Mahdi za ta fara wani rangadi, inda za ta ziyarci wasu daga cikin kasashen nahiyar Afirka, domin ganin an samu daidaiton baki a tsakanin kasashen nahiyar, kan yadda za a warware wannan matsala.
Daga cikin kasashen da ministar harkokin wajen za ta ziyarta har da Kenya, Rwanda da kuma Uganda, inda za ta gana da shugabannin wadannan kasashe.
342/