ABNA24 : Shugaba Aoun, ya bayyana hakan ne yayin da yake jagorantar wani taro na kan yadda za’a karfafa matakan yaki da safara muggan kwayoyi a tashohin ruwa dana sama na kasar.
Ya ce taron shi ne aiwatar da bukatar mahukuntan Riyad, bayan gano sama da muggan kwayoyi miliyan biyar a cikin kwalayen rumman da aka shiga dasu a birnin Djeddah.
Wanan dai na zuwa ne bayan haramcin shigar da kayayakin na Labanon zuwa Saudiyya ya fara aiki.
Saudiyya dai ta dau matakin ne saboda a cewarta yadda ake amfani da shigar da kayayakin na marmari da ‘ya ‘ya itatuwan na Labanon ana fataucin muggan kwayoyi zuwa cikin kasar.
Saudiyya dai it ace babbar abokiyar cinikin Labanon a kayan noma, kuma dakatar da sayan kayayakin babban nakaso ne ga Labanon wacce ke fama da matsalar tattalin arziki tun bayan fashewar data auku a tashr ruwan Beirut.
342/