25 Afirilu 2021 - 13:21
Yau Ce Ranar Yaki Da Zazzabin Cizon Sauro

Yau 25 ga watan Afrilu, ita ce ranar yaki da zazzabin cizon sauro a fadin duniya.

ABNA24 : Majalisar Dinkin Duniya ta ware 25 ga watan Afrilun kowace shekara domin zama ranar da ake bukin yaki da cutar zazzabin cizon sauro, ko malaria inda ake yin nazari kan matsaloli ko kuma nasarorin da aka samu fagen yaki da cutar.

A bikin na bana dai hukumar lafiya ta duniya, ta maida hankali ne kan nasarorin da kasashen duniya suka samu wajen kakkabe cutar dama wadanda ke kan kaiwa ga matakin, duk da kalubale da aka fuskanta na annobar korona.

WHO, ta ce kakkabe cutar da wasu kasashen sukayi manuniya ce ta cewa za’a iya cimma burin da aka sanya a gaba na kakkabe cutar mai kisa.

Zazzabin cizon sauro ko malaria da ake kamuwa da ita ta hanyar cizon sauro, na ci gaba da kasancewa cikin cututukan dake kisa a duniya, inda ko wacce shekara mutane sama da miliyan 200 ke kamuwa da ita sai kuma dubu 400 dake mutuwa sanadin cutar, kuma kimanin kashi biyu cikin uku na wadanda ta fi gallazawa yara ne ‘yan kasa da shekara biyar a cewar alkalumman na WHO.

342/