24 Afirilu 2021 - 13:37
​Nijar: Ana Bikin Ranar Hadin Kan ‘Yan Kasa Karo Na 26

A Jamhuriyar Nijar, yau ne 24 ga watan Afrilu ake gudanar da bikin ranar hadin-kan ‘yan kasa, ranar da ta samo asali daga yarjejeniyar zaman lafiya ta farko da aka kulla tsakanin ‘yan tawaye da gwamnatin kasar a irin wannan ranar ta shekarar 1995.

ABNA24 : An dai kulla yarjejeniyar ce a lokacin tsohon shugaban kasar marigayi Janar Ibrahim Ba’are Mainasara.

Wasu kasashen masu makobtaka da Nijar din ne da suka hada da Chadi, Mali, Burkina Faso da Aljeriya suka shiga tsakani a locacin rikicin inda kuma aka sansanta jituwa tsakanin Abzinawa da ke dauke da makamai da kuma gwamnatin ta Nijar.

Tun dai lokacin ne a zagayowar ranar ta 24 ga watan Afrilu ake gudanar da bukukuwa domin kara hada kan al’ummar kasar.

A bana dai ana gudanar bikin ne a garin Agadas dake arewacin kasar, kuma wannan shi ne karon na 26.

342/