19 Afirilu 2021 - 14:49
Iran Da Serbia Zasu Karfafa Alalar Dake Tsakaninsu

Kasashen Iran da Serbia, sun jadada mahimmancin karfafa alakar dake tsakaninsu a muhawarorin da suka shafi kasa da kasa.

ABNA24 : Yayin wata ganawa yau Lahadi da ministan harkokin wajen Serbia, Nikola Selaković, a Tehran, shugaban kasar Iran, Hassan Rohani, ya ce, yana da matukar mahimmacin bangarorin biyu Tehran-Belgrade su karfafa a alakar dake tsakaninsu.

Kasashen biyu za kuma su yi aiki tare domin murkushe annobar korona.

Shugaban Ruhani, ya ce, har kulun Iran, na goyan bayan hadin kan kasar Sarbia.

342/