17 Afirilu 2021 - 12:50
​Najeriya: Gwamnati Ta Dage Dokar Hana Rijistan Sabbin Layukan Tarho A Kasar

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada sanarwan cewa ta dage dokar hana rijistar sabbin layukan tarho a kasar, amma dole ne a yi amfani da lambar zama dan kasa wato NIN a rijistar.

ABNA24 : Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa dokar dage haramcin za ta fara aikin ne daga ranar 19 ga watan Afrilu da muke ciki, kuma an bukaci dukkan kamfanonin da za su saida sabbin layukan tarko a kasar su tabbatar da cewa sun bi dukkan sharuddan da gwamnatin tarayyar kasar ta sanya don rijistar sabbin layukan.

A ranar 9 ga watan Decemban da ya gabata ne gwamnatin tarayyar ta Najeriya ta bukaci dukkan kamfanin saida tarho na kasar su tsaida sayar da sabbin layuka, sannan su yi rijistan wadanda suka sayar tare da lambar ‘yan kasa wato NIN na duk wanda ya mallaki layin tarho a kasar.

Wannan dai ya na daga cikin shirin gwamnatin kasar na kyautata harkokin tsaro da kuma sawwaka ayyukan gwamnati.

342/