ABNA24 : Wannan bayanin ya fito yayin wata tattaunawa ta wayar tarho data gudana tsakanin shugaba Hassan Ruhani na Iran din da kuma Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya da yammacin jiya Laraba.
Bangarorin sun tabo batun yadda za’a gudunar da tattaunawar kwamitin kasuwanci na hadin guiwa na tsakanin kasashen biyu a cikin wata mai zuwa.
A cewar shugaba Ruhani, alakar dake tsakanin kasashen biyu zata taimaka gayen wajen karfara alakar amintaka da kuma taka mahimiyar rawa a yankin, musamman wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Shi kuwa shugaba Erdogan, ya taya al’ummar Iran da gwamnatin ta murna shiga wannan wata na Ramadan mai alfarma, tare da bayyana kyakyawar fatan gwamnatin Ankara, na karfafa alakarta da Jamhuriyar Musulinci ta Iran.
342/