15 Afirilu 2021 - 14:17
Za’a Gurfanar Da Blaise Compaore A Gaban Kotu Kan Kisan Thomas Sankara

An sanar da cewa za a gurfanar da tsohon shugaban ƙasar Burkina Faso, Blaise Compaore wanda a halin yanzu yake gudun hijira a ƙasar Ivory Coast a gaban ƙuliya don amsa zargin da ake masa na hannu cikin kisan gillan da aka yi wa tsohon shugaban ƙasar marigayi Thomas Sankara.

ABNA24 : Lauyoyin tsohon shugaba Sankaran ne suka sanar da hakan inda suka ce tuni aka tura da maganar zuwa wata kotun soji da ke birnin Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Fason bayan da aka tabbatar da cajin da ake yi wa waɗanda ake zargin ciki kuwa har da tsohon shugaba Compaore, shekaru 34 bayan wannan kisan gillan.

Ana zargin tsohon shugaban Compaore, wanda aka hamɓarar da shi daga mulki sakamakon boren gama gari da al’umma suka yi masa a ranar 31 ga watan Oktoban 2014, da barazana ga tsaron ƙasa, haɗa baki wajen kisan kai da kuma karɓar gawawwaki.

Tsawon mulkinsa na shekaru 27 dai Mr. Compaore ya ki gudanar da bincike da kuma hukunta waɗanda suke da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa marigayi Sankaran a ranar 15 ga watan Oktoban 1987 a lokacin yana da shekaru 38 a duniya.

Mutane 14 ne dai ake sa ran za a gurfanar a gaban kotun bisa wannan zargin.

342/